Mattiyu 19:16-22
16
To, fa, sai ga wani ya zo wurin Yesu ya tambaye shi ya ce, “Malam, wane abu mai kyau ne ya zama mini dole in yi don in sami rai madawwami?”
17
Yesu ya amsa ya ce, “Don me kake tambayata game da abin da yake mai kyau? Akwai Mai kyau Ɗaya kaɗai. In kana so ka sami rai madawwami, ka kiyaye dokokin nan.”
18
Mutumin ya yi tambaya ya ce, “Waɗanne?” Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Kada ka yi kisankai, kada ka yi zina, kada ka yi sata, kada ka yi shaidar ƙarya,
19
ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka,’ka kuma ‘ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’”
20
Saurayin ya ce, “Duk waɗannan na kiyaye. Me kuma ya rage mini?”
21
Yesu ya amsa ya ce, “In kana so ka zama cikakke, ka je, ka sayar da dukan dukiyarka ka kuma ba matalauta, za ka kuwa sami dukiya a sama. Sa’an nan ka zo, ka bi ni.”
22
Da saurayin ya ji haka, sai ya tafi rai a ɓace, don yana da arziki sosai.
Settings