Markus 9:30-37
30
Suka bar wurin suka bi ta Galili. Yesu bai so wani yă san inda suke ba,
31
gama yana koya wa almajiransa. Ya ce musu, “Za a ci amanar Ɗan Mutum, a ba da shi ga hannun mutane. Za su kashe shi, bayan kwana uku kuma zai tashi.”
32
Amma ba su fahimci abin da yake nufi ba, suka kuma ji tsoro su tambaye shi game da wannan.
33
Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?”
34
Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?
35
Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”
36
Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu,
37
“Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”
Settings