Markus 15:42-47
42
Ranar kuwa ita ce ranar Shirye-shirye (wato, ana kashegari Asabbaci). Saboda haka, da yamma ta yi, sai
43
Yusuf daga Arimateya, wani sanannen ɗan Majalisa, wanda dā ma yake jiran zuwan mulkin Allah, ya je wajen Bilatus ba tsoro, ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
44
Bilatus ya yi mamaki da ya ji cewa Yesu ya riga ya mutu. Sai ya kira jarumin ya tambaye shi ko Yesu ya riga ya mutu.
45
Da ya ji ta bakin jarumin cewa haka ne, sai ya ba wa Yusuf jikin.
46
Sai Yusuf ya kawo zanen lilin, ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi da lilin ɗin, sa’an nan ya sa shi a kabarin da aka fafe a cikin dutse. Sai ya gungura wani dutse ya rufe bakin kabarin.
47
Maryamu Magdalin da Maryamu uwar Yusuf sun ga inda aka kwantar da shi.
Settings