Markus 14:32-42
32
Suka tafi wani wurin da ake kira Getsemane, Yesu ya kuma ce wa almajiransa, “Ku zauna a nan, yayinda ni kuwa in yi addu’a.”
33
Ya tafi tare da Bitrus, Yaƙub da kuma Yohanna. Sai ya fara baƙin ciki da damuwa ƙwarai.
34
Sai ya ce musu, “Raina yana cike da baƙin ciki har ma kamar zan mutu. Ku dakata a nan ku yi tsaro.”
35
Sai ya yi gaba kaɗan, ya fāɗi a ƙasa, ya yi addu’a, ya ce in mai yiwuwa ne, a ɗauke masa wannan sa’a.
36
Ya ce, “Ya Abba,Uba, kome mai yiwuwa ne a gare ka. Ka ɗauke mini wannan kwaf. Amma ba abin da nake so ba, sai dai abin da kake so.”
37
Sai ya koma wajen almajiransa, ya same su suna barci. Ya ce wa Bitrus, “Siman, kana barci ne? Ka kāsa yin tsaro na sa’a ɗaya?
38
Ku yi tsaro, ku kuma yi addu’a, domin kada ku fāɗi cikin jarraba. Ruhu yana so, sai dai jiki raunana ne.”
39
Ya sāke komawa, ya maimaita addu’ar da ya yi.
40
Da ya dawo, ya sāke tarar da su suna barci, domin barci ya cika musu ido. Suka rasa abin da za su ce masa.
41
Da ya koma sau na uku, sai ya ce musu, “Har yanzu kuna barci, kuna hutawa ba? Ya isa! Lokaci ya yi. Duba an ba da Ɗan Mutum a hannun masu zunubi.
42
Ku tashi! Mu tafi! Ga mai bashe ni ɗin yana zuwa!”
Settings