Luka 7:18-20
18
Almajiran Yohanna suka gaya masa dukan waɗannan abubuwa. Sai ya kira biyu daga cikinsu,
19
ya aike su wurin Ubangiji, su tambaya su ce, “Kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?”
20
Da mutanen suka iso wurin Yesu, sai suka ce, “Yohanna Mai Baftisma ne ya aike mu wurinka, mu yi tambaya, ‘Ko kai ne wanda zai zo, ko kuma mu saurari wani dabam?’ ”
Settings