Skip to content
Luka 2:8-14

Luka 2:8-14

8
Akwai makiyaya masu zama a fili kusa da wurin, suna tsaron garkunan tumakinsu da dare.
9
Sai wani mala’ikan Ubangiji ya bayyana gare su, ɗaukakar Ubangiji kuma ta haskaka kewaye da su, suka kuwa tsorata ƙwarai.
10
Amma mala’ikan ya ce musu, “Kada ku ji tsoro. Na kawo muku labari mai daɗi na farin ciki mai yawa ne wanda zai zama domin dukan mutane.
11
Yau a birnin Dawuda an haifa muku Mai Ceto; shi ne Kiristi Ubangiji.
12
Wannan zai zama alama a gare ku. Za ku tarar da jariri a nannaɗe a zane kwance a kwami.”
13
Ba labari sai ga taron rundunar sama suka bayyana tare da mala’ikan, suna yabon Allah suna cewa,
14
“Ɗaukaka ga Allah a can cikin sama, a duniya kuma salama ga mutane waɗanda tagomashinsa yake bisansu.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options