Luka 2:1-5
1
A waɗancan kwanaki, Kaisar Augustus ya ba da doka cewa ya kamata a yi ƙidaya a dukan masarautar Roma.
2
(Wannan ce ƙidaya ta fari da aka yi a lokacin da Kwiriniyus yake gwamnar Suriya.)
3
Sai kowa ya koma garinsa don a rubuta shi.
4
Saboda haka Yusuf ma ya haura daga Nazaret a Galili zuwa Yahudiya, ya tafi Betlehem garin Dawuda, don shi daga gida da kuma zuriyar Dawuda ne.
5
Ya tafi can don a rubuta shi tare da Maryamu, wadda aka yi masa alkawari zai aura, tana kuwa da ciki.
Settings