Umurni Game da Karɓar Baƙi na Gaskiya
12
Sai Yesu ya ce wa wanda ya gayyace shi, “Lokacin da ka shirya biki ko liyafa, kada ka gayyaci abokanka, ko ’yan’uwanka, ko danginka, ko kuma maƙwabtanka masu arziki, gama in ka yi haka, suna iya gayyatarka, su biya maka alherin da ka yi musu.
13
Amma lokacin da ka kira biki, ka gayyaci matalauta, da guragu, da shanyayyu, da makafi.
14
Ta haka, za ka sami albarka. Ko da yake ba za su iya biyan ka ba, za a biya ka a ranar tashin masu adalci daga matattu.”
Settings