Skip to content
Firistoci 8:25-29

Firistoci 8:25-29

25
Ya ɗibi kitsen, da wutsiya mai kitse, da kuma dukan kitsen da ke kewaye da kayan ciki, da wanda ya rufe hanta, ƙodoji biyu da kitsensu da kuma cinya ta dama.
26
Sa’an nan daga cikin kwandon burodi marar yisti wanda yake a gaban Ubangiji, ya ɗauko dunƙulen burodi, da kuma guda da aka yi da mai, da kuma ƙosai; ya sa waɗannan a sassan kitsen, da kuma a cinya ta dama.
27
Ya sa waɗannan a hannuwan Haruna da ’ya’yansa, suka kuma kaɗa su a gaban Ubangiji a matsayin hadaya ta kaɗawa.
28
Sa’an nan Musa ya karɓe su daga hannuwansu ya ƙone a bagade a bisa hadaya ta ƙonawa a matsayin hadaya ta naɗi, mai daɗin ƙanshi, hadaya ce da aka ƙone da wuta ga Ubangiji.
29
Ya kuma ɗauki ƙirjin; rabon Musa na ɗan ragon naɗi, ya kaɗa shi a gaban Ubangiji, a matsayin hadaya ta kaɗawa, yadda Ubangiji ya umarce shi.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options