Firistoci 7:31-34
31
Firist zai ƙone kitsen a bisa bagade, amma ƙirjin zai zama na Haruna da ’ya’yansa maza.
32
Za ku ba da cinya ta dama ta hadaya don zumuncinku ga firist a matsayin baiko.
33
Ɗan Haruna da ya miƙa jini da kitsen hadaya ta salama, zai ɗauki cinyar tă zama rabonsa.
34
Daga hadaya ta salama ta Isra’ilawa, na ɗauki ƙirjin da aka kaɗa da kuma cinyar da aka miƙa, na ba da su ga Haruna firist da kuma ’ya’yansa maza a matsayin rabonsu na kullum daga Isra’ilawa.’ ”
Settings