Skip to content
Firistoci 4:27-31

Firistoci 4:27-31

27
“ ‘In wani memba a cikin jama’a ya yi zunubi ba da gangan ba, ya aikata ɗaya daga cikin abubuwan da Ubangiji ya umarta kada a yi, to, ya yi laifi.
28
Sa’ad da aka sanar da shi game da zunubin da ya yi, dole yă kawo akuya marar lahani a matsayin hadayarsa domin zunubin da ya yi.
29
Zai ɗibiya hannunsa a kan hadaya don zunubin yă kuma yanka ta a inda ake hadaya ta ƙonawa.
30
Sa’an nan firist zai ɗibi jinin da yatsarsa yă zuba a ƙahoni a bagaden hadaya ta ƙonawa, yă kuma zuba sauran jinin a ƙasan bagade.
31
Za a ɗebe kitsenta duka kamar yadda akan ɗebe kitsen hadaya ta salama. Firist zai ƙona shi a kan bagaden don ƙanshi mai daɗi ga Ubangiji. Ta haka firist zai yi kafara dominsa, za a kuwa gafarta masa.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options