Firistoci 3:8-10
8
Zai ɗibiya hannu a kan hadayarsa, yă yanka shi a gaban Tentin Sujada. Sa’an nan ’ya’yan Haruna maza za su yayyafa jinin dabbar a kowane gefe na bagade.
9
Daga hadaya ta zumuncin zai kawo, sai a miƙa waɗannan hadayu na ƙonawa ga Ubangiji a wuta, wato, kitsen, ƙibabbiya wutsiyar gaba ɗaya da ya yanka gab da ƙashin gadon baya, dukan kitsen da ya rufe kayan ciki, ko kuwa da suka shafe su,
10
da ƙodoji biyu tare da kitsen da yake kansu kusa da kwiɓi, da kuma murfin hanta waɗanda zai cire tare da ƙodoji.
Settings