- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Hukunci kan Takamaiman Fasikanci
Firistoci 20:9-21
9
“ ‘In wani ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, dole a kashe shi. Domin ya zagi mahaifinsa ko mahaifiyarsa, alhakin jininsa zai zauna a kansa.
10
“ ‘In mutum ya yi zina da matar wani, da matar maƙwabcinsa, dole a kashe su biyu da suka yi zinan.
11
“ ‘In mutum ya kwana da matar mahaifinsa, ya ƙasƙantar da mahaifinsa. Dole a kashe shi da macen, alhakin jininsu zai zauna a kansu.
12
“ ‘In mutum ya kwana da matar ɗansa, dole a kashe su biyun. Abin da suka yi haram ne; alhakin jininsu zai zauna a kansu.
13
“ ‘In mutum ya kwana da mutum kamar yadda ake kwana da mace, su biyun sun yi abin ƙyama. Dole a kashe su, alhakin jininsu zai zauna a kansu.
14
“ ‘In mutum ya auri ’ya da mahaifiyarta, mugun abu ne. Da shi da su, dole a ƙone su da wuta, saboda kada mugun abu yă kasance a cikinku.
15
“ ‘In mutum ya yi jima’i da dabba, dole a kashe shi, dole kuma ku kashe dabbar.
16
“ ‘In mace ta kusaci dabba don tă yi jima’i da ita, ku kashe macen da dabbar. Dole a kashe su; alhakin jininsu zai zauna a kansu.
17
“ ‘In mutum ya auri ’yar’uwarsa, ko ’yar mahaifinsa, ko kuwa ta mahaifiyarsa, suka kuma yi jima’i, abin kunya ne. Dole a raba su a idanun mutanensu. Ya ƙasƙantar da ’yar’uwarsa kuma za a nemi hakki daga gare shi.
18
“ ‘In mutum ya kwana da mace a lokacin al’adarta, duka biyunsu za a kore su daga cikin jama’arsu, gama sun karya ƙa’idodi a kan rashi tsarki.
19
“ ‘Kada ka yi jima’i da ’yar’uwar mahaifiyarka, ko ta mahaifinka, gama wannan zai ƙasƙantar da dangi na kurkusa, dukanku za ku ɗauki laifin.
20
“ ‘In mutum ya kwana da bābarsa, ya ƙasƙantar da kawunsa ke nan. Hakkin zai kasance a kansu, za su mutu babu ’ya’ya.
21
“ ‘In mutum ya auri matar ɗan’uwansa, aikin rashin tsabta ne, ya ƙasƙantar da ɗan’uwansa ke nan. Za su mutu babu ’ya’ya.
Settings