Tsallake zuwa abun ciki
Firistoci 19:19-29

Firistoci 19:19-29

19
“ ‘Ku kiyaye farillaina. “ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
20
“ ‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a ’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a ’yantar da ita ba.
21
Dole mutumin da ya kwana da ita yă kawo rago a ƙofar Tentin Sujada domin hadaya don laifi ga Ubangiji.
22
Da ragon hadaya don laifin ne firist zai yi kafara saboda mutumin a gaban Ubangiji saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta zunubinsa.
23
“ ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai ’ya’ya na ci, ku ɗauki ’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci. Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba.
24
A shekara ta huɗu, dukan ’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji.
25
Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin ’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku.
26
“ ‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa. “ ‘Kada ku yi duba ko sihiri.
27
“ ‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku.
28
“ ‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji.
29
“ ‘Kada ka ƙasƙantar da ’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options