Firistoci 19:17-37
17
“ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.
18
“ ‘Kada ka nemi yin ramuwa, ko ka riƙe wani cikin mutanenka a zuciya, amma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka. Ni ne Ubangiji.
19
“ ‘Ku kiyaye farillaina. “ ‘Kada ku sa dabbobin da ba iri ɗaya ba su yi barbara. “ ‘Kada ku yi shuki iri biyu a gonarku. “ ‘Kada ku sa rigar da aka saƙa da yadi iri biyu.
20
“ ‘In wani ya kwana da mace wadda take baiwa, wadda aka yi wa wani alkawari amma bai fanshe ta ba, ko kuwa ba a ’yantar da ita ba, dole a yi hukuncin da ya dace. Duk da haka ba za a kashe su ba, domin ba a ’yantar da ita ba.
21
Dole mutumin da ya kwana da ita yă kawo rago a ƙofar Tentin Sujada domin hadaya don laifi ga Ubangiji.
22
Da ragon hadaya don laifin ne firist zai yi kafara saboda mutumin a gaban Ubangiji saboda zunubin da ya yi, za a kuwa gafarta zunubinsa.
23
“ ‘Sa’ad da kuka shiga ƙasar kuka kuma shuka kowane irin itace mai ’ya’ya na ci, ku ɗauki ’ya’yan itatuwan nan a matsayi an hana ku ci. Shekara uku za ku ɗauka a matsayi an hana ku, ba za ku ci su ba.
24
A shekara ta huɗu, dukan ’ya’yansu za su zama tsarkakakku, hadaya ta yabo ga Ubangiji.
25
Amma a shekara ta biyar, za ku iya cin ’ya’yan itatuwan. Ta haka girbinku zai ƙaru. Ni ne Ubangiji Allahnku.
26
“ ‘Kada ku ci wani abinci tare da jini a cikinsa. “ ‘Kada ku yi duba ko sihiri.
27
“ ‘Ba za ka aske gefe-gefe na gashin kanka ba, ko ku aske gemunku.
28
“ ‘Kada ku tsattsaga jikunanku saboda matattu, ba kuwa za ku yi wa kanku zāne-zāne a jiki ba. Ni ne Ubangiji.
29
“ ‘Kada ka ƙasƙantar da ’yarka ta wurin mai da ita karuwa, in ba haka ba ƙasar za tă juya ga karuwanci tă kuma cika da mugunta.
30
“ ‘Ku kiyaye Asabbacina, ku kuma girmama wuri mai tsarkina. Ni ne Ubangiji.
31
“ ‘Kada ku juya ga masu duba, ko ku nemi shawarar bokaye, gama za ku ƙazantu ta wurinsu. Ni ne Ubangiji Allahnku.
32
“ ‘Ku miƙe tsaye a gaban tsofaffi, ku nuna bangirma ga waɗanda suka tsufa, ku kuma girmama Allahnku. Ni ne Ubangiji.
33
“ ‘Sa’ad da baƙo yana zama tare da ku a ƙasarku, kada ku wulaƙanta shi.
34
Dole ku ɗauki baƙon da yake zama tare da ku kamar haifaffe ɗan ƙasa. Ku ƙaunace shi kamar kanku, gama dā ku ma baƙi ne a Masar. Ni ne Ubangiji Allahnku.
35
“ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu.
36
Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.
37
“ ‘Ku kiyaye dukan farillaina da kuma dukan dokokina, ku kuma bi su. Ni ne Ubangiji.’ ”
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings