Makoki 2:18-22
18
Zuciyar mutane ta yi kuka ga Ubangiji. Ya bangon Diyar Urushalima, bar hawayenki su zuba kamar rafi dare da rana; kada ki huta, kada idanunki su huta.
19
Ki tashi, ki yi kuka cikin dare, dare na yi sai ki fara kuka; kina buɗewa Ubangiji zuciyarki. Ki ɗaga hannuwanki gare shi domin rayukan ’ya’yanki, waɗanda suka suma don yunwa a kan kowane titi.
20
“Ka duba, ka gani ya Ubangiji. Wane ne ka taɓa yi wa haka? Ko ya kamata uwaye su ci ’ya’yansu, ’ya’yan da suka yi reno? Ko ya kamata a kashe firistoci da annabawa a cikin haikalin Ubangiji?
21
“Matasa da tsofaffi duk suna kwanciya a cikin ƙurar tituna; an karkashe matasa da ’yan matana da takobi. Ka kashe su a ranar fushinka; ka kashe su ba tausayi.
22
“Kamar yadda kake yin gayyata a ranar biki, haka kake kawo mini tsoro a kowane gefe. A ranar fushin Ubangiji ba mai tserewa ba wanda zai tsira; maƙiyina ya kashe waɗanda na yi renonsu, na kuma lura da su.”
Settings