Makoki 1:18-22
18
“Ubangiji mai adalci ne, duk da haka na yi tawaye da umarninsa. Ku saurara, jama’a duka; ku dubi wahalar da nake sha. Samarina da ’yan matana duka sun tafi bauta.
19
“Na kira abokaina amma sun yashe ni. Firistocina da dattawana sun hallaka a cikin birnin yayinda suke neman abinci don kada su mutu da yunwa.
20
“Duba, Ubangiji, ka ga ƙuncin da nake ciki! Ina shan azaba a raina, ba ni da kwanciyar rai a cikin zuciyata, domin na yi tawaye sosai. A waje takobi na kisa; a ciki kuma akwai mutuwa.
21
“Mutane suna ji ina nishi da ƙyar, amma ba wanda zai yi mini ta’aziyya. Dukan maƙiyana sun ji wahalar da nake ciki; suna farin ciki da abin da ka yi. Ka kawo ranan nan da ka sanar domin su ma su zama kamar ni.
22
“Bari ka ga muguntarsu duka; ka yi musu yadda ka yi mini domin dukan zunubansu. Nishina da yawa kuma zuciyata ta gaji.”
Settings