Skip to content
Makoki 1:12-17

Makoki 1:12-17

12
“Ko wannan ba wani abu ba ne a wurinku, dukanku masu wucewa? Ku duba ku gani. Ko akwai wata wahala kamar irin wadda nake sha, wadda Ubangiji ya auko mini a cikin zafin fushinsa?
13
“Daga sama ya aiko da wuta, ya aiko ta cikin ƙasusuwana. Ya shimfiɗa raga a ƙafafuna ya juyo da ni. Ya bar ni ni kaɗai, sumamme dukan yini.
14
“Ya ɗaura zunubaina a wuyana; aka naɗe su a hannuwansa. Aka rataye su a wuyana Ubangiji ya kwashe ƙarfina. Ya bashe ni ga waɗanda suka fi ni ƙarfi.
15
“Ubangiji ya ƙi duk mayaƙan da suke tare da ni; ya sa wata runduna ta tayar mini ta kuma tattake samarina. Ubangiji ya tattake budurwa Diyar Yahuda kamar ’ya’yan inabi a wurin matsewa.
16
“Dalilin da ya sa nake kuka ke nan idanuna kuma suna ta zubar da hawaye. Babu wani a kusa da zai yi mini ta’aziyya, ba wanda zai sabunta ruhuna. ’Ya’yana sun zama fakirai domin maƙiyina ya yi nasara.”
17
Sihiyona ta miƙa hannunta, amma ba wani da zai yi mata ta’aziyya. Ubangiji ya umarta cewa maƙwabtansa za su zama maƙiyansa; Urushalima ta zama abar ƙyama a cikinsu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options