Makoki 1:8-11
8
Urushalima ta yi zunubi ƙwarai saboda haka ta zama marar tsarki. Dukan masu martaba ta sun raina ta, gama sun ga tsiraicinta; ita ma da kanta tana nishi da ƙyar ta kuma juya baya.
9
Ƙazantarta ta manne wa rigunanta; ba tă kula da nan gaba ba, fāɗuwarta kuwa babban abu ne; babu wanda zai yi mata ta’aziyya. “Duba, ya Ubangiji, ka ga wahalata, gama maƙiyi ya yi nasara.”
10
Maƙiya ya kwashe dukiyarta duka; ta ga mutanen da ba su san Allah ba sun shiga wuri mai tsarkinta waɗanda ka hana su shiga taron jama’arka.
11
Dukan mutanenta suna nishi da ƙyar suna neman burodi; sun sayar da dukiyarsu don su samu abinci don kada su mutu da yunwa. “Ubangiji, ka duba ka gani, gama an yashe ni.”
Settings