Mahukunta 9:34-45
34
Saboda haka Abimelek da dukan mutanensa suka tashi da dare suka ɓuya kusa da Shekem a ƙungiyoyi huɗu.
35
To, Ga’al ɗan Ebed ya riga ya fita waje yana tsaye a ƙofar birni daidai Abimelek da mayaƙansa suka fito daga inda suka ɓuya.
36
Sa’ad da Ga’al ya gan su, sai ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna gangarowa daga kan duwatsu!” Zebul ya ce, “Kana ɗaukan inuwan duwatsu kana ce mutane.”
37
Amma Ga’al ya sāke magana ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa daga tsakiyar filaye, kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen masu duba.”
38
Sa’an nan Zebul ya ce masa, “Ina bakin da ka yi ɗin, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa.’ Ba mutanen ne ka yi musu ba’a ba? Fita, ka yaƙe su mana!”
39
Saboda haka Ga’al ya fito da ’yan ƙasar Shekem suka yaƙi Abimelek.
40
Abimelek ya kore shi, mutane da yawa suka ji ciwo a yaƙin, har zuwa ƙofar birnin.
41
Abimelek ya zauna a Aruma, Zebul kuwa ya kori Ga’al da ’yan’uwansa daga Shekem.
42
Kashegari mutanen Shekem suka tafi gonaki, aka kuwa gaya wa Abimelek.
43
Saboda haka ya ɗauki mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, sa’an nan ya yi kwanto a gonakin. Sa’ad da ya ga mutanen suna fitowa daga birni, sai ya yi wuf ya fāɗa musu.
44
Abimelek da ƙungiyoyin da suke tare da shi suka yi maza suka yi tsaya a ƙofar birnin. Sa’an nan ƙungiyoyi biyu suka ruga suka fāɗa wa waɗanda suke a gonaki suka karkashe su.
45
Dukan yinin, Abimelek ya matsa yaƙi da birnin sai da ya cinye ta ya kuma kashe mutanenta. Sa’an nan ya hallaka birnin ya barbaza gishiri a kanta.
Settings