Skip to content
Mahukunta 9:26-41

Mahukunta 9:26-41

26
To, Ga’al ɗan Ebed ya tafi tare da ’yan’uwansa zuwa Shekem, ’yan ƙasarta kuwa suka dogara da shi.
27
Bayan sun tafi gonaki suka tattara inabi suka matse su, sai suka yi biki a haikalin allahnsu. Yayinda suke ci da sha, sai suka la’anci Abimelek.
28
Sa’an nan Ga’al ɗan Ebed ya ce, “Wane ne Abimelek, kuma wane ne Shekem, da za mu bauta masa? Shi ba ɗan Yerub-Ba’al ba ne, kuma ba Zebul ne mataimakinsa ba? Ku bauta wa mutanen Hamor, mahaifin Shekem! Me ya sa za mu bauta wa Abimelek?
29
Da a ce waɗannan mutane suna a ƙarƙashina mana! Da zan hamɓarar da shi. In ce wa Abimelek, ‘Ka tara dukan mayaƙanka!’ ”
30
Sa’ad da Zebul gwamnar birnin ya ji abin da Ga’al ɗan Ebed ya ce, sai ya fusata.
31
Asirce sai ya aiki manzanni wajen Abimelek, yana cewa, “Ga’al ɗan Ebed da ’yan’uwansa sun zo Shekem suna kuma zuga birnin sun tayar maka.
32
To, in dare ya yi, sai ka zo da mutanenka ku yi kwanto a filaye.
33
Kashegari da safe, sai ku tashi ku fāɗa wa birnin. Sa’ad da Ga’al da mutanensa suka faɗa maka, sai ka yi abin da ka iya yi da su.”
34
Saboda haka Abimelek da dukan mutanensa suka tashi da dare suka ɓuya kusa da Shekem a ƙungiyoyi huɗu.
35
To, Ga’al ɗan Ebed ya riga ya fita waje yana tsaye a ƙofar birni daidai Abimelek da mayaƙansa suka fito daga inda suka ɓuya.
36
Sa’ad da Ga’al ya gan su, sai ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna gangarowa daga kan duwatsu!” Zebul ya ce, “Kana ɗaukan inuwan duwatsu kana ce mutane.”
37
Amma Ga’al ya sāke magana ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa daga tsakiyar filaye, kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen masu duba.”
38
Sa’an nan Zebul ya ce masa, “Ina bakin da ka yi ɗin, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa.’ Ba mutanen ne ka yi musu ba’a ba? Fita, ka yaƙe su mana!”
39
Saboda haka Ga’al ya fito da ’yan ƙasar Shekem suka yaƙi Abimelek.
40
Abimelek ya kore shi, mutane da yawa suka ji ciwo a yaƙin, har zuwa ƙofar birnin.
41
Abimelek ya zauna a Aruma, Zebul kuwa ya kori Ga’al da ’yan’uwansa daga Shekem.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options