Mahukunta 9:23-30
23
sai Allah ya aiko da mugun ruhu tsakanin Abimelek da ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka ci amanar Abimelek.
24
Allah ya yi haka saboda kisan ’ya’ya saba’in na Yerub-Ba’al, don a ɗauki fansar jininsu a kan Abimelek ɗan’uwansu da kuma ’yan ƙasar Shekem, waɗanda suka taimake shi kisan ’yan’uwansa.
25
Cikin hamayya da shi waɗannan ’yan ƙasar Shekem suka sa mutane a kan tuddai don su yi kwanton ɓauna a kan su yi fashi ga duk wanda ya wuce a can, wannan fa ya kai kunnen Abimelek.
26
To, Ga’al ɗan Ebed ya tafi tare da ’yan’uwansa zuwa Shekem, ’yan ƙasarta kuwa suka dogara da shi.
27
Bayan sun tafi gonaki suka tattara inabi suka matse su, sai suka yi biki a haikalin allahnsu. Yayinda suke ci da sha, sai suka la’anci Abimelek.
28
Sa’an nan Ga’al ɗan Ebed ya ce, “Wane ne Abimelek, kuma wane ne Shekem, da za mu bauta masa? Shi ba ɗan Yerub-Ba’al ba ne, kuma ba Zebul ne mataimakinsa ba? Ku bauta wa mutanen Hamor, mahaifin Shekem! Me ya sa za mu bauta wa Abimelek?
29
Da a ce waɗannan mutane suna a ƙarƙashina mana! Da zan hamɓarar da shi. In ce wa Abimelek, ‘Ka tara dukan mayaƙanka!’ ”
30
Sa’ad da Zebul gwamnar birnin ya ji abin da Ga’al ɗan Ebed ya ce, sai ya fusata.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings