Skip to content
Mahukunta 8:13-21

Mahukunta 8:13-21

13
Sa’an nan Gideyon ɗan Yowash ya komo daga yaƙi ta Hanyar Heres.
14
Ya kama wani saurayin Sukkot ya tambaye shi, saurayin kuwa ya rubuta masa dukan sunayen shugabanni saba’in da bakwai na Sukkot, da dattawan garin.
15
Sa’an nan Gideyon ya zo ya ce wa mutanen Sukkot, “To, ga Zeba da Zalmunna, waɗanda kuka yi mini ba’a kuna cewa, ‘Ka kama Zeba da Zalmunna ko ne? Me zai sa mu ba mutanenka da suka gaji burodi?’ ”
16
Ya kwashe dattawan garin ya koya wa mutanen Sukkot hankali ta wurin hukunta su da ƙayayyuwan hamada.
17
Ya rushe hasumiyar Fenuwel ya kuma karkashe mutanen garin.
18
Sa’an nan ya ce wa Zeba da Zalmunna, “Waɗanne irin mutane ne kuka karkashe a Tabor.” Suka ce, “Mutane kamar ka ne kowane kamar ɗan sarki.”
19
Gideyon ya ce, “Waɗannan ’yan’uwana ne, ’ya’yan mahaifiyata. Muddin Ubangiji yana a raye, da a ce kun bar su da rai, da ba zan kashe ku ba.”
20
Da ya juya wajen Yeter, ɗan farinsa, sai ya ce, “Ka kashe su!” Amma Yeter bai zāre takobinsa ba, domin shi yaro ne kawai kuma yana tsoro.
21
Zeba da Zalmunna suka ce masa, “Zo, ka yi da kanka. ‘Yadda mutum yake haka ƙarfinsa.’ ” Ta haka Gideyon ya matso gaba ya kashe su, ya ɗauki kayan ado daga wuyar raƙumansu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options