Skip to content
Mahukunta 5:1

Mahukunta 5:1

Ana nuna aya 1 tare da mahallin da ke kewaye.
1
A wannan rana ce Debora da Barak ɗan Abinowam suka rera wannan waƙa.
2
“Sa’ad da ’ya’yan sarki a Isra’ila suka yi jagora, sa’ad da mutane suka niyya su ba da kansu, suna yabon Ubangiji!
3
“Ya sarakuna, ku ji! Ku saurara, ku masu mulki! Zan yi waƙa ga Ubangiji, zan yi waƙa; zan yi kaɗe-kaɗe ga Ubangiji, Allah na Isra’ila.
4
“Ya Ubangiji, sa’ad da ka bar Seyir, sa’ad da ka yi tafiya daga ƙasar Edom, ƙasa ta girgiza, sammai suka zubo, gizagizai sun zubo da ruwa.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options