Mahukunta 3:12-30
12
Isra’ilawa suka sāke aikata mugayen ayyuka a gaban Ubangiji, saboda sun aikata wannan mugunta sai Ubangiji ya ba wa Eglon sarkin Mowab ƙarfi a kan Isra’ila.
13
Da ya sami Ammonawa da Amalekawa suka haɗa hannu tare, sai Eglon ya tafi ya auka wa Isra’ila, suka ƙwace Birnin Dabino.
14
Isra’ilawa suka zama bayin Eglon sarkin Mowab shekara goma sha takwas.
15
Isra’ilawa suka sāke yin kuka ga Ubangiji, ya kuwa ba su mai ceto, Ehud, wani bahago, ɗan Gera daga kabilar Benyamin. Isra’ilawa suka aike shi da haraji wurin Eglon sarkin Mowab.
16
To, Ehud ya riga ya ƙera takobi mai kaifi biyu mai tsawo wajen kamu ɗaya da rabi, wanda ya yi ɗamara da shi a cinyarsa ta dama ƙarƙashin rigarsa.
17
Ya kai wa Eglon sarkin Mowab harajin, wanda yake mai ƙiba ne.
18
Bayan Ehud ya ba da harajin, sai ya sallame mutanen da suka ɗauko harajin.
19
A wajen gumaka kusa da Gilgal, shi kansa ya juya ya koma ya ce, “Ranka yă daɗe, ina da saƙo na asiri dominka.” Sarkin ya ce, “Ku ba mu wuri!” Sai dukan fadawansa suka fita.
20
Sai Ehud ya matso yayinda shi kuwa yake zaune shi kaɗai a ɗakin sama mai sanyi a fadansa ya ce, “Ina da saƙo daga wurin Allah dominka.” Sarki ya tashi daga kujerarsa,
21
Ehud ya kai hannun hagunsa, ya zaro takobi daga cinyar ƙafar damansa ya soki sarki a ciki.
22
Har ƙotar ma ta shige ciki, takobin kuma ya fito ta bayansa. Ehud bai zare takobin ba, kitse kuwa ya rufe shi.
23
Sa’an nan Ehud ya fita daga shirayin; ya rufe ƙofar ɗakin saman, ya kuma kulle su.
24
Bayan da ya tafi, bayin sarki suka zo suka tarar duk ƙofofin ɗakin sama suna kulle, suka ce, “Wataƙila yana bayan gari ne a ɗakin ciki.”
25
Suka yi ta jira har suka gaji. Da suka ga dai bai buɗe ƙofar ba, sai suka ɗauki mabuɗi, suka buɗe. Sai ga shugabansu a ƙasa matacce.
26
Yayinda suke fama jira, Ehud ya riga ya yi gaba. Ya bi ta wajen gumaka zuwa Seyira.
27
Da ya iso can, sai ya busa ƙaho a ƙasar tudu ta Efraim, Isra’ilawa kuma suka gangaro tare da shi daga tuddai, shi kuwa yana jagorarsu.
28
Ya umarce su ya ce, “Ku bi ni, gama Ubangiji ya ba Mowab abokin gābanku a hannunku.” Haka suka gangaro tare da shi suna mallaki mashigin Urdun da ta shiga zuwa Mowab, ba su yarda wani ya haye ba.
29
A lokacin sun kashe mutanen Mowab dubu goma, dukansu jarumawa da masu ji da ƙarfi; ba ko ɗaya da ya tsira.
30
A wannan rana aka mai da Mowab bayin Isra’ila, ƙasar kuwa ta sami zaman lafiya shekara takwas.
Settings