Mahukunta 2:1-9
1
Mala’ikan Ubangiji ya haura daga Gilgal zuwa Bokim ya ce, “Na hauro da ku daga Masar zuwa ƙasar da na rantse zan ba wa kakanninku. Na ce, ‘Ba zan taɓa tā da yarjejjeniyata da ku ba,
2
ku kuma kada ku shiga wata yarjejjeniya da mazaunan ƙasan nan, sai dai za ku rurrushe bagadansu.’ Duk da haka ba ku yi biyayya mini ba. Me ya sa kuka yi haka?
3
Saboda haka ina gaya muku cewa ba zan kore su a gabanku ba; za su zama muku ƙaya, gumakansu kuma za su zama muku tarko.”
4
Da mala’ikan Ubangiji ya faɗa wa dukan Isra’ilawa waɗannan abubuwa, sai mutane suka yi kuka mai zafi,
5
sai suka sa wa wannan wuri suna, Bokim. A nan suka miƙa hadaya a gaban Ubangiji.
6
Bayan Yoshuwa ya sallami Isra’ilawa, sai suka tafi don su mallaki ƙasar, kowa da nasa gādon.
7
Mutane suka bauta wa Ubangiji duk tsawon kwanakin Yoshuwa da na dattawan da suka rayu bayansa waɗanda suka ga manyan abubuwan da Ubangiji ya yi wa Isra’ila.
8
Yoshuwa ɗan Nun, bawan Ubangiji, ya mutu yana da shekara ɗari da goma.
9
Aka binne shi a ƙasar gādonsa, a Timnat Heres a ƙasar tudu ta Efraim, arewa da Dutsen Ga’ash.
Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.
Settings