Mahukunta 19:1-2
1
A kwanakin nan Isra’ila ba su da sarki. To, wani Balawe wanda yake zama a wani lungu na ƙasar tudu ta Efraim ya ɗauko wa kansa ƙwarƙwara daga Betlehem cikin Yahuda.
2
Amma ba tă yi aminci ba. Ta bar shi ta komo gidan mahaifiyarta a Betlehem, a Yahuda. Bayan ta zauna a can wajen wata huɗu,