Mahukunta 16:17-20
17
Saboda haka sai ya faɗa mata kome ya ce, “Ba a taɓa sa reza a kaina ba, domin ni Naziri ne keɓaɓɓe ga Allah tun haihuwa. In kuwa an aske kaina, ƙarfina zai rabu da ni, sai in zama kamar kowa.”
18
Da Delila ta gane ya gaya mata kome yanzu, sai ta aika saƙo zuwa ga shugabannin Filistiyawa ta ce, “Ku ƙara zuwa sau ɗayan nan, ai, ya gaya mini kome.” Saboda haka shugabannin Filistiyawa suka dawo tare da azurfa a hannuwansu.
19
Bayan ta sa shi ya yi barci a cinyarta, sai ta kira wani ya zo ya aske kitso guda bakwai nan a kansa, aka fara rinjayensa. Ƙarfinsa kuwa ya rabu da shi.
20
Sa’an nan ta yi ihu ta ce, “Samson ga Filistiyawa sun zo su kama ka!” Sai ya farka daga barci yana tsammani cewa, “Zan fita kamar dā in miƙe jikina.” Amma bai san cewa Ubangiji ya rabu da shi ba.
Settings