Mahukunta 12:8-15
8
Bayansa, Ibzan mutumin Betlehem, ya shugabanci Isra’ila.
9
Yana ’ya’ya maza talatin da ’ya’ya mata talatin. Ya ba da auren ’ya’yansa mata ga waɗanda ba daga dangi ba, ga ’ya’yansa maza kuwa ya kawo ’yan mata talatin su zama matansu waje da danginsa. Ibzan ya shugabanci Isra’ila shekara bakwai.
10
Sa’an nan Ibzan ya mutu, aka kuwa binne shi Betlehem.
11
Bayansa, Elon mutumin Zebulun, ya shugabanci Isra’ila shekara goma.
12
Sa’an nan Elon ya mutu, aka kuwa binne shi a Aiyalon a ƙasar Zebulun.
13
Bayansa, Abdon ɗan Hillel, daga Firaton, ya shugabanci Isra’ila.
14
Yana da ’ya’ya maza arba’in da ’yan taɓa kunne talatin, waɗanda suka hau jakuna saba’in. Ya shugabanci Isra’ila shekara takwas.
15
Sa’an nan Abdon ɗan Hillel ya mutu, aka kuwa binne shi a Firaton a Efraim, a ƙasar tudu ta Amalekawa.
Settings