Yoshuwa 6:22-25
22
Yoshuwa ya ce wa mutanen nan biyu waɗanda suka je leƙen asirin ƙasar, “Ku shiga gidan karuwan nan ku fitar da ita da duk waɗanda suke nata bisa ga alkawarin da kuka yi mata.”
23
Sai samarin waɗanda suka je leƙen asirin suka shiga suka fitar da Rahab, mahaifinta da mahaifiyarta, da ’yan’uwanta da duk abin da yake nata. Suka fitar da iyalinta gaba ɗaya suka sa su a wani wuri, ba a cikin masauƙin Isra’ilawa ba.
24
Sa’an nan suka ƙona birnin tare da dukan abin da yake ciki tatas, amma suka sa azurfa da zinariya da kayan tagulla da na ƙarfe a cikin ma’aji na haikalin Ubangiji.
25
Amma Yoshuwa ya bar Rahab karuwan nan bai kashe ta ba, ita da iyalinta da duk abin da yake nata, domin ita ta ɓoye mutanen da Yoshuwa ya aika Yeriko don su leƙo asirin ƙasar kuma ta zauna tare da Isra’ilawa har wa yau.
Settings