Yoshuwa 5:1-2
1
To, da dukan sarakunan Amoriyawa na yammancin Urdun, da dukan sarakunan Kan’aniyawan da suke bakin teku suka ji yadda Ubangiji ya busar da kogin Urdun a gaban Isra’ilawa, har sai da dukansu suka ƙetare, zuciyarsu ta narke, suka karaya sosai har ma suka rasa samun ƙarfin hali su fuskanci Isra’ilawa.
2
A lokacin nan Ubangiji ya ce wa Yoshuwa, “Ka yi wuƙaƙe na duwatsu ka yi wa Isra’ilawa kaciya.”
Settings