Skip to content
Yoshuwa 5:10-12

Yoshuwa 5:10-12

10
Da yamman rana ta goma sha huɗu ga wata, lokacin da suke a Gilgal a filin Yeriko, Isra’ilawa suka yi Bikin Ƙetarewa.
11
A kashegarin Bikin, a wannan rana, sai suka ci daga cikin amfanin ƙasar, burodi marar yisti da hatsin da aka gasa.
12
Kashegari bayan da suka ci amfanin ƙasar kuwa, Manna ta yanke, mutanen Isra’ila kuma ba su ƙara samunta ba. A wannan shekara suka fara cin amfanin ƙasar Kan’ana.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options