Yoshuwa 4:5-8
5
ya ce musu, “Ku je tsakiyar Urdun inda akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku yake. Kowannenku yă ɗauki dutse ɗaya a kafaɗarsa, bisa ga yawan kabilan Isra’ila,
6
yă zama muku alama. Nan gaba in yaranku suka tambaye ku suka ce, ‘Mece ce ma’anar kasancewar duwatsun nan a nan?’
7
Sai ku ce musu, ruwan Urdun ya yanke a gaban akwatin alkawari na Ubangiji, a lokacin da akwatin alkawarin ya ƙetare Urdun. Waɗannan duwatsu za su zama abin tuni ga Isra’ilawa har abada.”
8
Isra’ilawa kuwa suka yi yadda Yoshuwa ya umarce su. Suka ɗauki duwatsu guda goma sha biyu bisa ga yawan kabilan Isra’ila, yadda Ubangiji ya gaya wa Yoshuwa; suka tafi da su masauƙinsu, a can suka ajiye su.
Settings