Skip to content
Yoshuwa 23:6-13

Yoshuwa 23:6-13

6
“Ku yi ƙarfin hali, ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan abin da aka rubuta a cikin Littafin Dokoki na Musa, ba tare da kun juya hagu ko dama ba.
7
Kada ku haɗa kai da mutanen nan da suke zama cikinku; ba ruwanku da sunayen allolinsu, kada ku rantse da su. Kada kuwa ku bauta musu ko kuwa ku rusuna musu.
8
Sai dai ku riƙe Ubangiji Allahnku da kyau, yadda kuka yi har zuwa yanzu.
9
“Ubangiji ya kori manyan ƙasashe masu ƙarfi; har wa yau ba wanda ya iya cin ku da yaƙi.
10
Mutum ɗaya a cikinku ya isa yă sa mutane dubu nasu su gudu, domin Ubangiji Allahnku yana yaƙi dominku, kamar yadda ya yi alkawari.
11
Saboda haka sai ku kula da kanku sosai, ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku.
12
“Amma in kuka juya baya kuka zama abokai ga waɗanda suka ragu suke zama a cikinku a ƙasashen nan, har kuka yi auratayya da su, kuka haɗa kai da su,
13
ku tabbata cewa Ubangiji Allahnku ba zai kore muku mutanen ƙasashen nan ba, sai ma su zama muku dutsen tuntuɓe da tarko, za su zama bulala a bayanku, ƙayayyuwa a idanunku, har sai kun hallaka daga wannan ƙasa mai kyau wadda Ubangiji Allahnku ya ba ku.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options