Skip to content
Yoshuwa 23:1-9

Yoshuwa 23:1-9

1
An daɗe bayan da Ubangiji ya ba Isra’ilawa hutu daga dukan abokan gāban da suke kewaye da su. Yoshuwa kuwa ya tsufa, shekarunsa sun yi yawa,
2
sai ya aika a kira Isra’ilawa duka, dattawansu, shugabanninsu, alƙalansu, da manyan ma’aikatansu, ya ce musu, “Na tsufa, shekaruna kuwa sun yi yawa,
3
ku kanku kun ga dukan abubuwan da Ubangiji Allahnku ya yi da idanunku wa dukan ƙasashen nan, Ubangiji Allahnku shi ne wanda ya yi yaƙi dominku.
4
Ku tuna yadda na rarraba wa kabilanku ƙasashen nan su zama naku na gādo, dukan ƙasashen da suka rage, ƙasashen da na ci da yaƙi, tsakanin Urdun da Bahar Rum a yamma.
5
Ubangiji Allahnku kansa zai kore su a madadinku. Zai fafare su a gabanku, za ku kuwa mallaki ƙasarsu, yadda Ubangiji Allah ya yi muku alkawari.
6
“Ku yi ƙarfin hali, ku yi hankali, ku yi biyayya da dukan abin da aka rubuta a cikin Littafin Dokoki na Musa, ba tare da kun juya hagu ko dama ba.
7
Kada ku haɗa kai da mutanen nan da suke zama cikinku; ba ruwanku da sunayen allolinsu, kada ku rantse da su. Kada kuwa ku bauta musu ko kuwa ku rusuna musu.
8
Sai dai ku riƙe Ubangiji Allahnku da kyau, yadda kuka yi har zuwa yanzu.
9
“Ubangiji ya kori manyan ƙasashe masu ƙarfi; har wa yau ba wanda ya iya cin ku da yaƙi.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Reading Width 45 chars

Options