Skip to content
Yohanna 3:1-10

Yohanna 3:1-10

1
Akwai wani Bafarisiye mai suna Nikodimus, wani ɗan majalisar Yahudawa.
2
Ya zo wurin Yesu da dad dare ya ce, “Rabbi, mun sani kai malami ne daga Allah. Gama ba wanda zai iya yin waɗannan abubuwan banmamaki da kake yi in Allah ba ya tare da shi.”
3
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an sāke haihuwarsa.”
4
Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya za a haifi mutum sa’ad da ya tsufa? Tabbatacce ba zai sāke koma sau na biyu a cikin mahaifiyarsa don a haife shi kuma ba!”
5
Yesu ya amsa ya ce, “Gaskiya nake faɗa maka, ba wanda zai iya ganin mulkin Allah sai an haife shi ta wurin ruwa da kuma Ruhu.
6
Jiki yakan haifi jiki, amma Ruhu yana haifi ruhu.
7
Kada ka yi mamaki da na ce, ‘Dole ne a sāke haifarku.’
8
Iska takan hura zuwa inda take so. Kai kakan ji motsinta, sai dai ba ka iya sanin inda take fitowa ko kuwa inda za ta. Haka yake ga duk wanda aka haifa ta wurin Ruhu.”
9
Nikodimus ya yi tambaya ya ce, “Yaya wannan zai yiwu?”
10
Yesu ya ce, “Kai ma da kake malami na Isra’ila, ba ka fahimci waɗannan abubuwa ba?
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options