Skip to content
Yohanna 21:9-19

Yohanna 21:9-19

9
Da suka sauka, sai suka ga garwashin wuta a can da kifi a kai, da kuma ’yan burodi.
10
Yesu ya ce musu, “Ku kawo waɗansu kifin da kuka kama yanzu.”
11
Sai Siman Bitrus ya hau ya jawo abin kamun kifin gaci. Ya cika da manyan kifi, 153, amma duk da yawansun nan abin kamun kifin bai tsintsinke ba.
12
Yesu ya ce musu, “Ku zo ku karya kumallo.” Ba wani daga cikin almajiran da ya yi karambanin tambayarsa, “Wane ne kai?” Sun san cewa Ubangiji ne.
13
Yesu ya zo, ya ɗauki burodin ya ba su, haka kuma kifin.
14
Wannan fa shi ne sau na uku da Yesu ya bayyana kansa ga almajiransa bayan an tashe shi daga matattu.
15
Da suka gama ci, sai Yesu ya ce wa Siman Bitrus, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske fiye da waɗannan?” Ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Ciyar da ’ya’yan tumakina.”
16
Har wa yau Yesu ya ce, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata da gaske?” Ya amsa ya ce, “I, Ubangiji, ka san cewa ina sonka.” Yesu ya ce, “Lura da tumakina.”
17
Sau na uku ya ce masa, “Siman ɗan Yohanna, kana ƙaunata?” Sai Bitrus ya ɓata rai saboda Yesu ya tambaye shi sau na uku, “Kana ƙaunata?” Ya ce, “Ubangiji ka san kome duka; ka san cewa, ina ƙaunarka.” Yesu ya ce, “Ciyar da tumakina.
18
Gaskiya nake faɗa maka, sa’ad da kake saurayi kakan yi wa kanka sutura ka tafi inda ka so; amma sa’ad da ka tsufa za ka miƙa hannuwanka, wani dabam yă yi maka sutura yă kai ka inda ba ka so.”
19
Yesu ya faɗi wannan ne, don yă nuna irin mutuwar da Bitrus zai yi yă ɗaukaka Allah. Sa’an nan ya ce masa, “Bi ni!”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options