Yohanna 20:1-10
1
Da sassafe a ranar farko ta mako, tun da sauran duhu, Maryamu Magdalin ta tafi kabarin ta kuwa tarar an kawar da dutsen daga bakin kabarin.
2
Sai ta zo da gudu wajen Siman Bitrus da ɗayan almajirin, wanda Yesu yake ƙauna, ta ce, “Sun ɗauke Ubangiji daga kabarin, ba mu kuma san inda suka sa shi ba!”
3
Sai Bitrus da almajirin nan suka nufi kabarin.
4
Dukansu biyu suna gudu, amma ɗayan almajirin ya tsere wa Bitrus ya kuma fara kai kabarin.
5
Ya sunkuya ya duba ciki ya ga ƙyallayen lilin ne kwance a can amma bai shiga ba.
6
Sa’an nan Siman Bitrus, wanda yake bayansa, ya iso ya kuwa wuce cikin kabarin. Ya ga ƙyallayen lilin kwance a can,
7
haka ma zanen binnewar da aka naɗe kan Yesu da shi. Zanen a naɗe yake shi kaɗai, a keɓe da lilin ɗin.
8
A ƙarshe sai almajirin nan, wanda ya kai kabarin da farko, shi ma ya shiga. Ya gani ya kuma gaskata.
9
(Har yanzu ba su fahimci Nassin nan da ya ce lalle ne Yesu yă tashi daga matattu ba.)
10
Sai almajiran suka koma zuwa inda suke zama.
Settings