Yowel 2:21-24
21
Kada ki ji tsoro, ya ƙasa; ki yi murna ki kuma yi farin ciki. Tabbatacce Ubangiji ya yi abubuwa masu girma.
22
Kada ku ji tsoro, ya ku namun jeji, gama wuraren kiwo sun yi kore shar. Itatuwa suna ba da ’ya’yansu; itacen ɓaure da na inabi suna ba da amfaninsu.
23
Ku yi murna, ya ku mutanen Sihiyona, ku yi farin ciki cikin Ubangiji Allahnku, gama ya ba ku ruwan bazara cikin adalci. Yakan aika muku yayyafi a yalwace, na bazara da na kaka, kamar dā.
24
Masussukai za su cika da hatsi; randuna za su cika da sabon ruwan inabi da mai suna zuba.
Settings