Ayuba 32:6-14
6
Sai Elihu ɗan Barakel mutumin Buz ya ce, “Ni ƙarami ne a shekaru, ku kuma kun girme ni; shi ya sa na ji tsoro na kāsa gaya muku abin da na sani.
7
Na ɗauka ya kamata ‘shekaru su yi magana; ya kamata yawan shekaru su koyar da hikima.’
8
Amma ruhun da yake cikin mutum, numfashin Maɗaukaki shi ne yake ba shi ganewa.
9
Ba tsofaffi ne kaɗai suke da hikima ba, ba masu yawan shekaru ne suke gane abin da yake daidai ba.
10
“Saboda haka nake ce muku, ku saurare ni; ni ma zan gaya muku abin da na sani.
11
Na jira sa’ad da kuke magana, na ji muhawwararku lokacin da kuke neman abin da za ku faɗa,
12
na saurare ku da kyau. Amma ba waninku da ya nuna Ayuba yana da laifi; ba ko ɗayanku da ya amsa muhawwararsa.
13
Kada ku ce, ‘Mun sami hikima; Allah ne kaɗai yake da ikon yin nasara da shi ba mutum ba.’
14
Amma ba da ni Ayuba ya yi gardama ba kuma ba zan amsa masa da irin amsarku ba.
Settings