Ayuba 27:2-6
2
“Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.
3
Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
4
bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.
5
Ba zan taɓa yarda cewa kuna da gaskiya ba; har in mutu, ba zan daina kāre mutuncina ba.
6
Zan ci gaba da adalcina, ba zan fasa ba; lamirina ba zai taɓa yashe ni ba, dukan kwanakin raina.
Settings