1
Ayuba kuwa ya ci gaba da magana,
2
“Na rantse da Allah mai rai, wanda ya danne mini gaskiyata, Maɗaukaki, wanda ya sa nake cikin ɗacin rai.
3
Muddin ina da rai a cikina kuma numfashin Allah yana cikin hancina,
4
bakina ba zai faɗi mugun abu ba, harshena kuma ba zai yi ƙarya ba.