Ayuba 12:7-12
7
“Amma ka tambayi dabbobi, za su kuma koya maka, ko kuma tsuntsayen sararin sama kuma za su gaya maka.
8
Ko ka yi magana da duniya, za tă kuma koya maka, ko kuma ka bar kifin teku su sanar da kai.
9
Wane ne cikin waɗannan bai san cewa hannun Ubangiji ne ya yi wannan ba?
10
Ran kowace halitta yana a hannunsa, haka kuma numfashin dukan ’yan adam.
11
Ko kunne ba ya gwada kalmomi kamar yadda harshe yake ɗanɗana abinci?
12
Ko ba a wurin tsofaffi ake samun hikima ba? Ba tsawon rai yana kawo ganewa ba?
Settings