Skip to content
Ayuba 12:1-6

Ayuba 12:1-6

1
Sai Ayuba ya amsa,
2
“Ba shakka ku ne mutanen nan, hikima za tă mutu tare da ku!
3
Amma ni ma ina da hankali kamar ku; ba ku fi ni ba. Wane ne bai san duk waɗannan abubuwan ba?
4
“Na zama abin dariya ga abokaina, ko da yake na yi kira ga Allah ya kuwa amsa mini, duk da haka suka yi mini riya ko da yake ni mai adalci ne kuma marar laifi!
5
Mutanen da ba su da damuwa suna jin daɗin ganin waɗanda suke dab da fāɗuwa.
6
Amma wurin zaman ’yan fashi yana nan ba mai damunsu, waɗanda kuma suke saɓa wa Allah suna zamansu lafiya, har ma da masu ɗaukar allahnsu a hannuwansu.
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options