Ayuba 12:17-25
17
Yakan sa mashawarta su zama marasa hikima yă kuma sa wawaye su zama masu shari’a.
18
Yana cire sarƙar da sarakuna suka ɗaura yă kuma ɗaura musu wata tsumma a kwankwaso.
19
Yakan ƙasƙantar da firistoci yă kuma tumɓuke masu ikon da aka kafa tun da daɗewa.
20
Yana sa amintattun mashawarta su yi shiru yakan kawar da hikimar dattawa.
21
Yakan sa masu iko su ji kunya yă kuma ƙwace ƙarfin masu ƙarfi.
22
Yana buɗe abubuwan da suke cikin duhu yă kuma kawo haske a wuraren da ba haske;
23
yana sa al’ummai su zama manya, sai kuma yă hallaka su; yana sa al’ummai su ƙasaita, yă kuma watsar da su.
24
Yana hana shugabannin duniya ganewa; Ya bar su su yi ta makuwa, su ruɗe, su ɓata.
25
Suna lallube cikin duhu ba haske; yă sa su yi ta tangaɗi kamar bugaggu.
Settings