Irmiya 7:5-11
5
In dai kuka canja hanyoyinku da ayyukanku kuma kuna aikata adalci da junanku,
6
in ba ku zalunci baƙo, maraya ko gwauruwa ba kuma in ba ku zub da jinin marar laifi a wannan wuri ba, in kuma ba ku bi waɗansu alloli da za su cuce ku ba,
7
to, zan bar ku ku zauna a wannan wuri, a ƙasar da na ba kakanninku har abada abadin.
8
Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani.
9
“ ‘Za ku yi sata da kisa, ku yi zina da rantsuwar ƙarya, kuna ƙone turare wa Ba’al kuna kuma bin waɗansu allolin da ba ku sani ba,
10
sa’an nan ku zo ku tsaya a gabana a wannan gida, wanda ake kira da Sunana, kuna cewa, “An cece mu,” mun dace mu aikata waɗannan abubuwa banƙyama?
11
Wannan gidan da ake kira da Sunana ya zama kogon ’yan fashi ne a gare ku? Amma ina kallo! In ji Ubangiji.
Settings