Irmiya 6:1-5
1
“Ku gudu neman mafaka, mutanen Benyamin! Ku gudu daga Urushalima! Ku busa ƙaho a Tekowa! Ku ba da alama a Bet-Hakkerem! Gama masifa tana zuwa daga arewa, mummunar hallaka ce kuwa.
2
Zan hallaka Diyar Sihiyona, kyakkyawa da kuma mai laulayi.
3
Makiyaya da garkunansu za su taso mata; za su kafa tentunansu kewaye da ita, kowanne yana lura da sashensa.”
4
“Mu shirya don yaƙi da ita! Ku tashi, bari mu fāɗa mata da tsakar rana! Amma, kaito, rana tana fāɗuwa, inuwar yamma kuwa sai ƙaran tsawo take.
5
Saboda haka ku tashi, bari mu fāɗa mata da dare mu rurrushe kagaranta!”
Settings