Skip to content
Irmiya 42:7-19

Irmiya 42:7-19

7
Bayan kwana goma sai maganar Ubangiji ta zo wa Irmiya.
8
Saboda haka ya kira Yohanan ɗan Kareya da dukan shugabannin sojoji waɗanda suke tare da shi da dukan jama’a daga ƙarami zuwa babba.
9
Ya ce musu, “Ga abin da Ubangiji, Allah na Isra’ila, wanda kuka aike ni gare shi don in gabatar da kukanku, yana cewa,
10
‘In kuka zauna a wannan ƙasa, zan gina ku ba zan kuwa rushe ku ba; zan dasa ku ba kuwa zan tumɓuke ku ba, gama ina baƙin ciki a kan masifar da na aukar a kanku.
11
Kada ku ji tsoron sarkin Babilon, wanda kuke tsoro a yanzu. Kada ku ji tsoronsa, in ji Ubangiji, gama ina tare da ku zan kuma cece ku daga hannuwansa.
12
Zan nuna muku jinƙai don yă nuna muku jinƙai ya kuma maido da ku ƙasarku.’
13
“Amma fa, in kuka ce, ‘Ba za mu zauna a wannan ƙasa ba,’ ta haka kuka kuma nuna rashin biyayya ga Ubangiji Allahnku,
14
in kuma kuka ce, ‘A’a, za mu tafi mu zauna a Masar, inda ba za mu ga yaƙi ko mu ji ƙarar ƙaho ko mu ji yunwa ba,’
15
to, ku ji maganar Ubangiji, ya raguwar Yahuda. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘In kun ƙudura ku tafi Masar kuka kuma tafi kun zauna a can,
16
takobin da kuke tsoro zai same ku a can, kuma yunwar da kuke tsoro za tă bi ku zuwa Masar, a can kuwa za ku mutu.
17
Tabbatacce, duk waɗanda suka ƙudura suka tafi Masar su zauna a can za su mutu ta wurin takobi, yunwa da annoba; ba ko ɗayansu zai tsira ko ya kuɓuta wa masifar da zan aukar a kansu.’
18
Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki, Allah na Isra’ila, yana cewa, ‘Kamar yadda na kwararo fushina da hasalata a kan mazaunan Urushalima, haka kuma zan kwararo fushina a kanku sa’ad da kuka tafi Masar. Za ku zama abin la’ana da abin tsoro, abin ƙyama da abin ba’a; ba za ku ƙara ganin wannan wuri ba.’
19
“Ya ku raguwar Yahuda, Ubangiji ya ce muku, ‘Kada ku je Masar.’ Ku tabbatar da wannan. Na gargaɗe ku yau
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options