Skip to content
Irmiya 35:2-10

Irmiya 35:2-10

2
“Ka tafi wurin iyalin Rekabawa ka gayyace su su zo a ɗaya daga cikin ɗakunan da suke gefe a gidan Ubangiji ka kuma ba su ruwan inabi su sha.”
3
Sai na tafi don in kawo Ya’azaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da ’yan’uwansa da kuma dukan ’ya’yansa maza, dukan iyalin Rekabawa.
4
Na kawo su cikin gidan Ubangiji, a cikin ɗakin ’ya’yan Hanan ɗan Igdaliya maza mutumin Allah. Ɗakin ne kusa da ɗakin fadawa, wanda yake bisa na Ma’asehiya ɗan Shallum mai tsaron ƙofa.
5
Sai na ajiye ƙwarya cike da ruwan inabi da waɗansu kwaf a gaban iyalin Rekabawan na kuma ce musu, “Ku sha ruwan inabin.”
6
Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi.
7
Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’
8
Mun yi biyayya da kome da kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu. Mu ko matanmu ko ’ya’yanmu maza da mata ba mu taɓa shan ruwan inabi ba
9
ba mu kuma gina gidaje mu zauna a ciki ba ko mu yi gonakin inabi, gonaki ko hatsi ba.
10
Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options