Skip to content
Irmiya 35:1-11

Irmiya 35:1-11

1
Ga maganar da ta zo wa Irmiya daga wurin Ubangiji a lokacin mulkin Yehohiyakim ɗan Yosiya sarkin Yahuda.
2
“Ka tafi wurin iyalin Rekabawa ka gayyace su su zo a ɗaya daga cikin ɗakunan da suke gefe a gidan Ubangiji ka kuma ba su ruwan inabi su sha.”
3
Sai na tafi don in kawo Ya’azaniya ɗan Irmiya, ɗan Habazziniya, da ’yan’uwansa da kuma dukan ’ya’yansa maza, dukan iyalin Rekabawa.
4
Na kawo su cikin gidan Ubangiji, a cikin ɗakin ’ya’yan Hanan ɗan Igdaliya maza mutumin Allah. Ɗakin ne kusa da ɗakin fadawa, wanda yake bisa na Ma’asehiya ɗan Shallum mai tsaron ƙofa.
5
Sai na ajiye ƙwarya cike da ruwan inabi da waɗansu kwaf a gaban iyalin Rekabawan na kuma ce musu, “Ku sha ruwan inabin.”
6
Amma sai suka amsa suka ce, “Ba ma shan ruwan inabi, domin kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu cewa, ‘Ko ku, ko zuriyarku kada ku sha ruwan inabi.
7
Haka kuma ba za ku gina gidaje, ku dasa iri ko ku nome gonakin inabi ba; kada ku kasance da wani daga cikin waɗannan abubuwa, amma dole kullum ku zauna a tentuna. Ta haka za ku yi dogon rai a cikin ƙasar baƙuncinku.’
8
Mun yi biyayya da kome da kakanmu Yehonadab ɗan Rekab ya umarce mu. Mu ko matanmu ko ’ya’yanmu maza da mata ba mu taɓa shan ruwan inabi ba
9
ba mu kuma gina gidaje mu zauna a ciki ba ko mu yi gonakin inabi, gonaki ko hatsi ba.
10
Mun yi rayuwarmu a cikin tentuna mun kuma yi biyayya ƙwarai da kowane abin da kakanmu Yehonadab ya umarce mu.
11
Amma da Nebukadnezzar sarkin Babilon ya kawo wa ƙasan nan hari, sai muka ce, ‘Ku zo, dole mu tafi Urushalima don mu tsira daga Babiloniyawa da kuma sojojin Arameyawa.’ Saboda haka ne muke a Urushalima.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options